Amurka ta ci baya a tsarin dimokuradiyya

Amurka ta shiga cikin jerin kaasashen da suka samu koma baya a tsarin dimokuradiyya a karon farko, kamar yadda rahoton Cibiyar Nazarin Tsarin Dimokradiyya ta kasa-da-kasa ya ce.

A duniya baki daya, sama da daya cikin mutum hudu suna rayuwa ne karkashin dimokuradiyya duk da koma bayan da ake samu, adadin da ya haura sama da biyu cikin uku yayin da ake samun karuwar gwamnatocin da ba sa mutunta dimokradiayya a rubuce, a cewar cibiyar.

A cikin rahotonta mai taken samun koma baya karon farko a Amaurka, ta ce a wannan shekarar an sanya kasar  ne sakamakon bayanan da suka tattara tun daga 2019.

Amurka wadda ta kasance ja-gaba a tsarin dimokuradiyya, har ma ta inganta ayyukanta wajen gudanar da mulki ba tare da nuna fifiko ba, musamman wajen yakar rashawa da kuma inganta shirin sauraron koken ‘yan kasar a 2020, amma duk da haka, an samu koma baya ga ‘yancin dan adam haka ma tsarin bincikar gwamnati na nuna cewa akwai matsaloli masu tsauri, in ji Alexander Hudson, wani mawallafin rahoton, da ya shaida wa AFP.

Wani sauyi mai cike da tarihi ya zo a shekarar 2020-21 lokacin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya nuna shakku kan sahihancin sakamakon zaben 2020 a Amurka, in ji rahoton.

Bugu da kari, Hudson ya yi nuni da raguwar ingancin ‘yancin yin taro yayin zanga-zangar shekarar 2020 biyo bayan kisan da ‘yan sanda suka yi wa George Floyd.

IDEA ta alakanta rahotonta kan shekaru 50 da aka dauka akan tsarin dimokuradiyya a cikin kasashe kusan 160, inda aka raba su zuwa rukuni uku wato mulkin dimokuradiyya ciki har da wadanda aka samu koma baya da suka hada da gwamnatocin kama-karya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *