Sojin Sudan sun amince Hamdok ya koma mukaminsa bayan yarjejeniya

Jagoran gwamnatin sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan da Firaminista Abdalla Hamdok sun cimma yarjejeniyar da za  maido da Firaministan karagar mulki tare da sakin jagororin fararen hula da ake tsare da su tun bayan juyin mulkin da soji suka yi, kamar yadda masu shiga Tsakani suka sanar a yau Lahadi.

A ranar 25 ga watan Oktoba Burhan ya kakaba dokar ta-baci a kasar, kana ya kifar da gwamnati mai mulki a wani mataki da ya taka wa shirin mika mulki ga zababben shugaban farar hula, ya kuma janyo caccaka daga kasashen duniya tare da haddasa gagarumar zanga-zanga.

Babban mai shiga Tsakani na Sudan, Fadlallah Burma, wanda shine mukaddashin shugaban jam’iyyar Umma a kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an cimma yarjejeniyar maido da Hamdock kan mukaminsa sakamakon ganawa tsakanin Janar din da Hamdok da kuma jam’iyyun siyasa na kasar da kungiyoyin fararen hula.

Wata kungiyar masu shiga tsakani ta Sudan da ta kunshi malaman manyan makarantu da ‘yan siyasa, wadanda tun da aka fara rikicin kasar suka shiga tattaunawa ne suka fitar da sanarwar yarjejeniyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *