Liverpool ta lallasa Arsenal da ci 4-0

Kungiyar Liverpool ta lallasa Arsenal a gasar Firimiya ta Ingila da ci 4-0 abinda ya kawo karshen wasanni 10 da kungiyar tayi ba tare da an samu nasara akan ta ba.

‘Yan wasan gaba guda 3 na Liverpool da suka hada da Sadio Mane da Diogo Jota da kuma Mohamed Salah sun jefa kwallo guda-guda kafin daga bisani Takumi Minamino ya jefa ta 4.

Wannan nasara ta taimakawa Liverpool komawa matsayi na biyu a teburin Firimiya da maki 25, yayin da Chelsea ke sahun gaba da maki 29.

Yayin karawar an samu tada jijiyoyin wuya tsakanin Mikel Arteta na Arsenal da Jurgen Kloop na Liverpool lokacin da Sadio Mane ya rafke dan wasan Arsenal, abinda ya sa alkalin wasa ya nunawa manajojin guda biyu katin gargadi.

Bayan kammala wasan Arteta yace tabbas Liverpool tafi su taka leda, domin sun barar da wasan ne tun a mintuna 15 da fara shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *