Hatsarin kwale-kwale ya hallaka ‘Yan Mata 7 a Jigawa

A Najeriya wasu ‘Yan mata 7 ne suka nutse a ruwa bayan da wani kwale-kwale da suke cikin ya kife a jihar Jigawa da ke arewacin kasar.

Kakakin ‘yan sandan jihar Jigawa Lawan Shiisu yace ‘Yan mata 10 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 12, na kan hanyarsu ta komawa gida cikin dare bayan wani biki kafin iftila’in ya rutsa da su.

“An ceto uku daga cikinsu yayin da wasu bakwai… aka ruwaito sun mutu,” in ji Shiisu.

‘Yan matan, wadanda suka kosa su koma gida da karfe 12:15 na dare, sun yanke shawarar jan kwale-kwale da suka samu a bakin kogin da kansu ba tare da wani matuki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.