Dakarun Isra’ila sun kashe mutumin da ya kai hari kan ‘yan kama-wuri-zauna

Dakarun Isra’ila sun harbe wani Bafalasdine har lahira bayan da ya kai harin bindiga da wuka har ya kashe wani Bayahude  dan kama wuri zauna tare da raunata wasu 3, ciki har da jami’an ‘yan sanda 2.

Da safiyar Lahadin nan ne aka yi wannan fito na fito da makamai a kofar Bab al-Silsila ta shigamasallacin al-Aqsa a gabashin Birnin Kudus da Isra’ila ta mamaye.

Kafofin yada labaran yankin sun ce mutumin da ya kai wannan hari, mazaunin sansanin ‘yan gudun hijira na Shuafat ne a Birnin Kudus, kuma sunansa Fadi Abu Shkheidem mai shekaru 42.

Wadanda suka samu raunin da suka hada da ‘yan sanda 2 suna asibiti ana yi musu magani, kamar yadda cibiyar  kula da lafiya ta Hadassah ta bayyana a wata sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.