Kotu ta wanke matashin da ya harbe mutane 2 har lahira a Amurka

Kotu ta wanke Kyle Rittenhouse, matashin nan, Ba’amurke da harbe mutane 2 har lahira yayin zanga zangar adawa da cinzalin ‘yan sanda a Win sconsin a shekarar da ta gabata daga dukkanninn zarge zarge da ake mai a jiya Juma’a, bayan wani zaman kotu mai cike da sarkakiyar siyasa da rarrabuwar kawuna.

Kotu ba ta same Rittenhouse,  mai shekaru 18, da laifin kisa da gangan ba, da ma sauran zarge zargen da ake masa sakamakon harbe harben da ya yi a Kenosha na Winsconsin a shekarar 2020.

Rittenhouse, wanda ya yi ikirarin cewa ya aikata abin da ya aikata ne domin kare kansa, ya yi ta karkarwa da kuka a yayin da ake karanta hukunkcin, daga bisani ya rungume lauyansa, kana ya fita daga kotun a guje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *