Dalilan da suka sa Amurka ta cire Najeriya cikin masu hana addini

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana dalilan da suka kasar ta cire sunan Najeriya cikin jerin kasashen da ke hana mutane ‘yancin gudanar da addininsu a duniya.

Yayin da yake jawabi a Abuja Blinken ya ce sun dauki matakin ne sakamakon kwararan shaidun da suka samu da ke nuna cewar kasar ba ta katsalandan kan harkokin addini.

Blinken ya ce Najeriya da Amurka suna fuskantar kalubale daban-daban cikinsu har da matsalar tsaron da ta shafi kowacce kasa.

Sakataren ya ce kasashen biyu sun yanke hukuncin ci gaba da aiki tare wajen ganin sun shawo kan matsalar tsaron da ke tsakaninsu, yayin da ya bayyana cewar shugaban Amurka Joe Biden zai fayyace shirin gwamnatin kasar dangane da Afirka a yau juma’a.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da ziyarar da kuma yadda Amurka ta cire sunan Najeriya cikin jerin kasashen da ke hana mutane gudanar da addininsu.

Buhari ya ce gwamnati ba ta hana wani dan kasa gudanar da addininsa kamar yadda doka ta tanada.

A farkon wannan mako Amurka ta sanar da cire sunan Najeriya daga jerin kasashen da ke tirsasa wa mabiya wani addini wajen hana su ‘yancinsu, yayin da ta sanya sunan kasar Rasha a ciki.

Sauran kasashen da ke cikin jerin wadanda ke hana ‘yancin addinin sun hada da China da Myanmar da Eritrea da Koriya ta Arewa da Pakistan da Saudi Arabia da Tajikistan da kuma Turmenistan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *