Sakataren wajen Amurka Antony Blinken na ziyara a Najeriya

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a yau alhamis ya sauka birnin Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya domin ganawa da mahukuntan kasar.

Ziyarar dai na zuwa ne a wani yanayi da bayanai ke nuni da cewa yanzu haka Amurka na fatan sake bitar alaka a fannoni da dama tsakaninta da Najeriya, musammam batutuwan da suka shafi kare hakkin dan adam da kuma kyautata tsarin dimokuradiyya.

Kasar da ta fi kowace yawan al’umma a nahiyar Afirka, a wasu lokatu Najeriya na fuskantar suka daga mahukuntan kasar Amurka saboda da rashawa da ta yi wa sha’anin mulkin kasar katutu, sai kuma tauye hakkin bil’adama musamman daga shekarar da ta gabata lokacin da jami’an tsaro suka murkushe boren EndSARS.

A lokacin da ya gurfana gaban kwamitin harkokin wajen majalisar dokokin Amurka, shugaban kwamitin Bob Menendez, ya shaida wa Antony Blinken cewa ya zama wajibi Amurka ta sake bitar yarjeniyoyi da dama da ke tsakaninta da Najeriya.

To sai dai a jajibirin wannan ziyara ta Mista Blinken, Amurka ta sanar da cire Najeriya daga cikin jerin sunayen kasashen da ke hana jama’a ‘yancin yin addini.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *