Buhari na goyan bayan kato-bayan-kato – Gbajabiamila

Shugaban Majalisar tarayyar Najeriya Femi Gbajabiamila yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na goyan bayan zaben ‘yar tinke wanda aka fi sani da kato-bayan-kato wajen tsayar da ‘Yan takarar zabe kamar yadda majalisun kasar suka amince da ita a matsayin dokar kasa.

Bayan ganawa da shugaban a fadar sa, Gbajabiamila yace sabuwar dokar da ake jiran Buhari ya rattaba hannu akan ta zata bada damar aiwatar da ita domin baiwa matasa damar shiga a dama da su a cikin dimokiraiyar kasar.

Shugaban majalisar yace nan gaba kadan za’a kaiwa shugaban kasa gyaran da suka yiwa dokar zaben domin sanya hannu akai

Gbajabiamila yace tun kafin yin dokar sun san cewar Buhari na goyan bayan wannan tsari, domin da shi yayi amfani wajen tsayawa takarar zaben da ya kaishi karagar mulki.

Tuni dai wannan dokar ta haifar da cece kuce tsakanin ‘yan majalisun tarayya da gwamnonin jihohi wadanda suka fito karara suke adawa da ita.

Gwamnonin wadanda suka yi kaurin suna wajen amfani da wakilan dake tsayar da ‘yan takara domin amincewa da bukatun su, sun ce basa goyan bayan sabuwar dokar, yayin da suke cewa zata haifar da matsala a shirin zaben kasar.

Masu sharhi akan siyasar Najeriya da matasa sun bayyana farin cikin su da wannan sabuwar dokar wadda suke cewar zata budewa mutane da dama kofar shiga siyasa da kuma tsayawa takara sabanin yadda gwamnoni ke dauki dora a shekarun baya.

Wasu na kallon wannan tsari a matsayin wanda zai baiwa Yan Najeriya damar zabin abinda suke so.

2 Replies to “Buhari na goyan bayan kato-bayan-kato – Gbajabiamila”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *