Wutar gas ta kashe mutane a jihar Lagos

An samu asarar rayukan mutane akalla biyar sakamakon fashewar tukunyar iskar gas a unguwar Mushin da ke jihar Lagos ta Najeriya.

Lamarin ya fau ne a sanyin safiyar ranar Talatar nan da misalin karfe 9 , yayin da wasu da dama suka jikkata.

Babban jami’in Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya reshen jihar Lagos, Ibrahim Farinloye ya tabbatar da aukuwar lamarin a wani gidan sayar da iskar gas din da ke kusa da kasuwar Ladipo.

Tuni aka yi nasarar kashe wutar gas din, yayin da jami’an kashe gobara da ‘yan sanda da sauran jami’an agajin gaggawa suka halarci wurin aukuwar hatsarin.

Darektar Hukumar Kashe Gobara, Misis Margaret Adeseye ta ce, za su gudanar da bincike domin gano musabbabin fashewar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.