Tagwayen hare-haren kunar bakin wake sun hallaka mutane 3 a Uganda

Akalla Mutane 3 aka tabbatar da mutuwar su yayin da wasu 33 suka samu raunuka daban daban lokacin da wasu hare haren kunar bakin wake guda biyu suka ritsa da jama’a a birnin Kampala da ke kasar Uganda.

‘Yan Sanda a Uganda sun danganta tashin bama baman da kungiyar Allied Democratic Forces wanda ke kai hare hare a Gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar congo da kuma ake bayyana cewar tana alaka da kungiyar IS.

Kakakin Yan Sandan kasar Fred Enanga yace wasu Yan kunar bakin wake guda 2 akan baburan haya da ake kira boda-boda suka tada bama baman kusa da kofar shiga majalisar dokoki, abinda yayi sanadiyar kashe wani mai tafiya, yayin da aka kai hari na 3 kusa da wurin binciken ababan hawar dake kusa da tashar Yan Sanda, abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane 2.

Tada bam din a tsakiyar birnin Kampala da ake hada hadar kasuwanci ya faru ne bi da bi bayan karfe 10 na safiyar yau, yayin da sassan jikin mutane ya tarwatse a wurin.

Babu wata sanarwar daukar alhaki dangane da hare haren, amma kakakin Yan Sandan birnin Enanga ya danganta harin da ayyukan ta’addanci na cikin gida.

Jami’in ya kuma ce sun daike hari na 3, inda suka kwace kayan tada bam a gidan wani da ake zargin dan kunar bakin wake ne, wanda aka raunata bayan harbin da aka masa, yayin da suka sanar da ci gaba ad farautar sauran mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *