Sheikh Gumi ya gina wa Fulanin daji makaranta

Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya gina wata makaranta domin ilmantar da ‘ya’yan Fulani makiyaya a wani kauye da ke kusa da dajin Kahoto a jihar Kaduna.

Malamin ya ce, Gidauniyar Masallacin Sultan ce ta ware kudaden gina makarantar mai suna Cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio.

Malamamin ya ce, za su samar da makamantan wannan makaranta a daukacin sassan Najeriya, yana mai shawartar gwamnati da ta kashe kudi wajen gina irin wannan makaranta da malamai domin ilmantar da makiyaya a maimakon ta rika kashe biliyoyin kudi wajen sayo makaman soji domin yaki da ‘yan bindiga.

Malamin ya kara da cewa, ya gana da ‘yan bindigar kuma sun shaida masa cewa, a shirye suke su ajiye makamansu tare da rungumar zaman lafiya muddin za a bai wa ‘ya’yansu ilimi da kuma samar musu da kayayyakin more rayuwa.

Sheikh Gumi ya sha ganawa da ‘yan bindigar a dazukan da suke rayuwa, lamarin da ya janyo masa yabo da kuma caccaka daga ‘yan Najeriya.

One Reply to “Sheikh Gumi ya gina wa Fulanin daji makaranta”

Leave a Reply

Your email address will not be published.