Za mu magance matsalar Guinea da kanmu – Doumbouya

Shugaban Mulkin Sojin Guinea, Mamady Doumbouya ya ce, kasarsa za ta iya magance matsalarta da kanta. Kalamansa na zuwa ne kwanaki kalilan da Kungiyar ECOWAS ta tsananta matsayarta kan gwamnatin kasar.

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta dakatar da Guinea a matsayin mambar kungiyar tare da lafta wa manyan sojojinta takunkumai saboda juyin mulkin da suka yi a ranar 5 ga watan Satumba wanda ya kawo karshen shugabancin Alpha Conde.

ECOWAS ta bukaci sojojin da su gaggauta sakin Conde mai shekaru 83 da suka yi masa daurin talala tun bayan tunbuke shi daga kujerar mulkinsa.

Tuni Kungiyar Ta Yammacin Afrika ta nada jakada zuwa Guinea tare da bukatar gudanar da zabe cikin watanni shida domin mayar da mulki ga farar hula.

A wata hirarsa da aka watsa ta kafar talabijin a ranar Asabar da ta gabata,  Doumbouya ya ce, suna bai wa Conde cikakkiyar kulawa, amma al’ummar Guinea ce kadai za ta iya fayyace makomarsa.

Doumbouya wanda aka rantsar a matsayin shugaban rikon kwarya a watan jiya, ya ce, yana adawa da matakin ECOWAS na nada jakada na musamman da kuma wa’adin gudanar da zabe cikin watanni shida.

Doumbouya ya kara da cewa, suna da cikakkiyar basirar magance matsalarsu domin kuwa kasarsu ba ta cikin rikici, hasali ma kasa ce wadda makomarta ke hannunta a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *