Faransa ta gargadi Birtaniya kan yi mata katsalanda

Faransa ta gargadi Birtaniya game da yi mata kastalandan kan yadda za ta yi da bakin-haure, a dai-dai lokacin da rashin jituwa ke kara ta’azzara a tsakanin kasashen biyu game da batun kwararar bakin haure zuwa Turai.

Faransan ta yi wannan gargadin ne a daidai lokacin da batun kwararar bakin-haure zuwa Turai ke sake daukar sabon salo yayin da kowacce kasa ke zargin ‘yar uwarta da laifin.

Faransa ta ce, babu yadda za a yi ta bari Birtaniya ta ci gaba da amfani da sunanta wajen cimma wata bukata ta siyasa a cikin gida.

Tun da fari Birtaniya ce ta fara zargin Faransan da bai wa bakin-haure dama wajen kwarara cikinta, bayan ratsawa zuwa Turai, yayin da take ganin Faransan ba ta daukar wani mataki na hana hakan.

Sai dai kuma da ta ke mayar da martani, Faransan ta ce, laifin Birtaniya ne game da yadda bakin- haure ke kwarara a don haka ta shawarce ta kan ta mayar da hankali kan matsalolinta na cikin gida ba wai yi mata kastalandan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *