Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta samu nasara akan takwararta ta kasar Liberia da ci 2-0 a wasan neman tikitin zuwa cin kofin duniya da zai gudana a Qatar a shekara mai zuwa.
Victor Osimhen da Ahmed Musa suka jefawa Najeriya kwallayen ta guda biyu a karawar da ta baiwa kungiyar Super Eagles damar ci gaba da zama a sahun gaba a teburin rukuni na C na nahiyar Afirka.
Wannan ya nuna cewar Najeriya na da maki 12 a saman tebur, yayin da Cape Verde na matsayi na 2 da maki 10, sai kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dake matsayi na 3 da 4, yayin da Liberia ke matsayi na 4 da maki 3.
Karawar da za’ayi tsakanin Najeriya da Cape Verde a birnin Lagos ranar talata itace zata bada damar sanin kasar da zata lashe wannan rukuni na wasanni da kuma samun damar zuwa wasannin karshe na neman tikitin.
Wasu daga cikin wasannin da akayi a karshen mako sun nuna cewar Kamaru ta lallasa Malawi da ci 4-0, yayin da Cote d’Ivoire ta doke Mozambique da ci 3-0.

Equatorial Guinea ta samu nasarar doke Tunisia da ci 1-0, kuma wannan shine karo na farko da aka samu nasara akan Tunisia a birnin Malabo, yayin da Zambia ta doke Mauritania da ci 4-0.
Ya zuwa wannan lokaci kasashen Masar da Mali da Morocco da Senegal sun samu tikitin zuwa zagaye na gaba, yayin da ayau lahadi ake saran kasashe irin su Ghana da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo ko kuma Jamhuriyar Benin su shiga cikin jerin su.