Kasashen duniya 200 sun kulla yarjejeniya a taron yanayi

Kasashen duniya 200 da suka hadu a taron sauyin yanayi na COP26 a Glasgow na kasar Scotland sun amince da wata yarjejeniya a ranar Asabar don hanzarta yaki da dumamar yanayi, amma ba tare da ba da tabbacin cimma burin rage matakin zuwa 1.5 ° na ma’aunin C ba, haka zalika taron ya Karkare ba tare da amsa bukatar kasashe masu fama da talauci dake nemem dauki ba.

An zargi kasashe masu arziki da gazawa a taron na COP26 wajen samar da kudaden da ake bukata ga kasashe da ke cikin hadarin fari, tunbasar teku, gobara da guguwa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da kansa ya lura da raunin wannan “Yarjejeniyar Glasgow”, yana mai gargadin cewa “har yanzu bala’in yanayi na nan daram”,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *