Faransa da Belgium sun samu tikitin zuwa Qatar

Kasar Faransa ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniyar da zai gudana shekara mai zuwa a kasar Qatar, sakamakon gagarumar nasarar da ‘Yan wasan ta suka samu akan kungiyar Kazakhstan da ci 8-0.

‘Dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe ya jefawa kwallaye guda 4 daga cikin 8 da kasar sa ta jefa a wasan da akayi, yayin da Karem Benzema ya jefa guda 2, sai kuma Rabiot da Antoine Griezmann da suka jefa guda-guda.

Wannan nasara ta baiwa Faransa damar samun tikitin da zai kaita Qatar domin kare kambin da ta samu shekaru 4 da suka gabata.

Lucas Hernandez da Kylian Mbappe bayan lashe gasar cin kofin duniya FRANCK FIFE AFP/File

Ita ma kasar Belgium ta samu tikitin zuwa gasar bayan ta doke Estonia da ci 3-1 a karawar da suka yi jiya asabar.

Christian Benteke da Carasco da kuma Thorgan Hazard suka jefawa kasar su kwallayen da suka samu nasara a karawar da suka yi da Estonia.

Lucas Paqueta a tsakiya yana murnar jefa kwallo wa kasar sa tare da Vinicius Junior da Neymar NELSON ALMEIDA AFP

Sauran kasashen da suka samu tikitin zuwa wasan yanzu haka sun hada da Denmark da Brazil da Jamus da kuma Qatar mai masaukin baki.

Wasu daga cikin wasannin da aka kara asabar din nan a nahiyar Turai sun nuna cewar Turkiya ta doke Gibraltar da ci 6-0, Wales ta lallasa Belarus da ci 5-1, Netherlands ta tashi 2-2 da Montenegro, sai kuma Norway da tayi canjaras 0-0 da kasar Latvia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *