Buhari ya jajantawa iyalan Janar da wasu sojoji da ISWAP ta kashe

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan rasuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da wasu sojojin kasar da mayakan ISWAP su kashe a arewa maso gabashin kasar.

An kashe jami’an ne a wani harin kwantan bauna da mayakan kungiyar IS da ke yankin yammacin Afirka (ISWAP) suka kai musu.

Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce marigayin ya yi gagarumin sadaukarwa da ba a saba gani ba saboda  kokarin taimakawa ‘yan uwansu wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Buhari, wanda ya bukaci babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya karbi ta’aziyyarsa da ta kasa, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka yi shahada.

“Najeriya ta yi rashin jaruman sojoji. Ina gaishe da jajircewarsu. Allah Ya Jikan su da Rahma. Janar Zirkusu ya bar mana bakin ciki da bacin rai”

Rohatanni daga Najeriyar na cewa akalla sojojin kasar bakwai ne aka kashe a wasu hare-haren kwanton bauna biyu da mayakan jihadi da ke da alaka da IS suka kai a arewa maso gabashin kasar, kamar yadda majiyoyin soja suka sanar ranar Asabar.

Ana samun yawaitan hare-haren kwanton bauna da mayanakan ISWAP ke  kai wa ayarin motocin a yankin arewa maso gabashin kasar inda sojoji ke fafatawa don kawo karshen rikicin da ‘yan kishin Islama suka kwashe shekaru 12 ana yi wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula sama da 40,000.

A ranar Asabar sojoji hudu ciki har da wani kwamandan soji suka mutu a lokacin da mayakan na ISWAP suka yi musu kwanton bauna yayin da suke tafiya don ba da taimako yayin wani harin da mayakan jihadi suka kai a garin Askira Uba na jihar Borno, in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

Sai kuma wasu sojoji uku da aka kashe a ranar Juma’a yayin da mayakan ISWAP suka yi wa ayarin motocin kwantan bauna a jihar Yobe mai makwabtaka da jihar, kamar yadda wasu majiyoyin soja biyu suka bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published.