Amurka ta gargadi China kan matsin lamba ga Taiwan gabanin taron Biden-Xi

Amurka ta gargadi China kan matsin lambar da take wa Taiwan, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar ranar Asabar a daidai lokacin da shugabannin mayan kasashen duniyar biyu ke shirin gudanar da wani taro da aka dade ana jira.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya tattauna da ministan harkokin wajen China Wang Yi inda ya nuna damuwarsa kan ci gaba da matsin lambar soji da diflomasiyya da kuma na tattalin arziki da China ke yi wa Taiwan.

Shugaba Joe Biden da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping za su gudanar da wani taron ta fasahar bidiyo a yammacin ranar Litinin agogon.

Blinken da Wang sun tattauna a ranar Jumma’a, inda suka tabo shirye-shiryen taron kasashen biyu, inda aka ce sakataren ya bukaci Beijing da ta shiga tattaunawa mai ma’ana, don warware batutuwan da suka shafi mashigin ruwa cikin lumana, kuma ta hanyar da ta dace da buri da moriyar jama’ar Taiwan. “

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *