Pakistan na duba yiwuwar yafe wa Taliban

Gwamnatin Pakistan ta fara tattaunawa da ‘ya’yan tsagin kungiyar Taliban da ta haramta a kasar a wani yunkuri na baiwa mambobinta damar mika wuya don yafe musu tare da aje makamansu.

Ma’aikatar Yada Labaran Pakistan ta ce, tuni ta fara tattaunawa da shugabancin kungiyar ta TTP ko kuma Tahreek-e-Taliban Pakistan wadda ke biyayya ga kungiyar Taliban da ta kwace iko da Afghanistan watanni biyu da suka gabata.

Ta wani sako da Ministan Yada Labaran Pakistan Fawad Chaudary ya sanar yayin zantawa da shi ta kafar talabijin ya ce kungiyar yanzu haka ta yi alkawarin tsagaita wuta na tsawon lokaci don fara tattaunawa da mahukuntan kasar.

Galibin mayakan kungiyar ta TTP dai bayanai sun ce, sun yi sansani a Afghanistan gab da iyakar Pakistan daga gabashi wato yankin tsaunuka, bayan fatattakarsu daga kasar shekaru 10 da suka gabata.

Kungiyar ta TTP ko kuma Pakistan Taliban ana ganin ita ke da alhakin sanya kasar a rikici tsakanin shekarun 2007 bayan da fusatattun masu kishin Islama suka samar da ita don kalubalantar Amurka a yakinta da ayyukan ta’addanci.

Acewar Fawwad Chaudary tattaunawa da kungiyar wadda har zuwa yanzu za ta ci gaba da zama a haramtacciyarta zai gudana ne bisa tanadin hakan daga kundin tsarin mulkin kasar.

Ministan ya ce sun duba bukatu masu alaka da manufofin kasa, zaman lafiya tsaro tattalin arziki da sauran muhimman bangarori gabanin amincewa da fara tattaunawa da kungiyar wadda ta taimaka wajen hambarar da mulki a Afghanistan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *