Amurka ta bude iyakokinta ga baki bayan shafe watanni 20 a rufe

Kasar Amurka ta bude iyakokin ta na sama da kasa ga baki ‘yan kasashen waje wadanda suka karbi allurar rigakafi, bayan rufe iyakokin da tayi na tsawon watanni 20 domin yaki da annobar Korona.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kafa dokar hana baki shiga kasar a farkon shekarar 2020, wadda ta kuma samu goyan bayan shugaba Joe Biden da ya gaje shi domin dakile yaduwar cutar.

A watan Maris na shekarar 2020 shugaba Trump ya sanar da rufe iyakokin kasar ga baki daga kasashe dama cikin su harda masu zuwa daga Turai da Birtaniya da China da India da kuma Brazil.

Wannan haramci na Amurka ya gamu da suka musamman daga kasashen Turai da kuma makociyar ta dake Canada da Mexico.

Sanarwar gwamnatin Amurka ta ce janye haramci zai shafi baki daga kasashe sama da 30, amma kuma hukumomi za su ci gaba da sanya ido domin tabbatar da cewar masu shiga kasar sun karbi allurar rigakafi sau biyu da kuma shaidar cewar basa dauke da cutar Korona.

Umurnin ya kuma kunshi cewar duk mai bukatar shiga Amurkar sai yi nuna shaidar gwajin da aka masa kwanaki 3 kafin tafiyar sa kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *