‘Yan sanda sun ceto mutanen da ‘yan bindiga suka sace daga jami’ar Abuja

‘Yan sandan Najeriya sun samu nasarar ceton dukkanin mutanen da ‘yan bindiga suka sace daga rukunin gidajen ma’aikatan Jami’ar birnin Abuja a ranar Talata.

Da safiyar ranar Talatar da ta gabata 2 ga watan Nuwamba gungun ‘yan bindiga suka kutsa kai bangaren gidajen ma’aikatan jami’ar Abuja suka kuma yi awon gaba da mutane shida, ciki har da Farfesa biyu.

Kafin kubutar da su dai sai da ‘yan bindigar suka nemi a biya su kudin fansar da ya kai naira miliyan 300, kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa dasu.

Sai dai da safiyar yau Juma’a, wani jami’in jami’ar ta UNIABUJA ya sanar da ceto ma’aikatan nasu ba kuma tare da biyan kudin fansa ba.

Zalika rundunar ‘yan sandan dake kula da shiyyar ta hannun mai Magana da yawunta DSP Josephine Adeh, ta tabbatar da sakin mutanen ba tare da yin karin bayani ba, illa kama wasu dake da hannu a cikin ta’asar da tace an yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *