Xavi ya zama sabon kocin Barcelona

Barcelona na shirin sanar da sake kulla yarjejeniya da tsohon dan wasanta Xavi Hernandez, wanda a wannan karon zai koma gareta a matsayin mai horas da ‘yan wasanta.

An kai wannan matakin ne bayan da aka cimma yarjejeniya tsakanin Barcelona da Al Sadd, kungiyar da Xavin ke horaswa a kasar Qatar.

Cikin sanarwar da ta fitar kungiyar ta Qatar ta ce Barcelona ta biya kudin sayen yarjejeniyar da ta rage tsakaninta Xavi, wanda ke horar da ‘yan wasanta a Qatar tun shekarar 2019.

Yanzu haka dai ma’abota duniyar wasanni na dakon ganin yadda Xavi zai maido da karsashin tsohuwar kungiyarsa, zuwa makamancin lokacin da suke a matsayin ‘yan wasa.

Xavi Hernandez, tare da Lionel Messi yayin murnar jefa kwallo a ragar Sevilla. Ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar 2014.

A lokacin da yake taka leda dai ana yi wa Xavi lakabi da ‘Maquina’, abinda ke nufi Inji da turancin Spain, dalilin kasancewarsa dan wasan tsakiya wanda ya yi fiye da fice wajen sarrafa kwallon kafa har tsawon shekaru goma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *