Farashin abinci a duniya ya yi tsada mafi tsanani cikin shekaru 10

Majalisar Dinkin Duniya ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a duniya a watan Oktoban da ya gabata, mafi tsananin tsadar da aka gani cikin shekaru 10.

Hukumar samar da abinci da kuma bunkasa noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO ta ce alkaluman farashin kayan abincin ya karu ne da kashi 3 bisa 100 a watan na Oktoba inda ya kai maki 133.2 bisa ma’auni.

A bangaren kayan lambu dai hukumar ta FAO ta ce farashinsu ya karu ne da kashi 9.6 mataki mafi girma da aka taba gani.

Ƙididdigar farashin hatsi kuwa ya karu ne da kashi 3.2 bisa 100, wanda ya haifar da ribar kashi biyar cikin 100 akan alkama, a yayin da adadinta da aka samarwa ya ragu sakamakon matakin rage nomanta da manyan kasashe suka yi.

A dunkule dai farashin kayayyakin abincin da ya karu sau uku cikin watanni ukun da suka gabata, abinda ya sanya hauhawar farashin zama mafi tsanani da aka gani tun bayan watan Yulin shekarar 2011.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *