Sabon kocin Tottenham Antonio Conte ya fara jagorantar kungiyar da kafar dama, bayan da ya samu nasara kan Vitesse da kwallaye 3-2 a wasan farko da kungiyar ta fafata a karkashinsa na gasar Europa a daren ranar Alhamis.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Tottenham ta sanar da Conte a matsayin sabon kocinta da ya maye gurbin wanda ta kora Nuno Espirito.
A mintuna 45 na farkon wasan na daren Alhamis da suka fafata sai da magoya bayan Tottenham suka yi tsayuwar ban girma ga Conte ganin yadda cikin mintuna 28 kungiyar tasa dake wasa a gida ta samu nasarar jefa kwallaye 3 a ragar Vitesse.
A shekarar 2016 dai Antonio Conte ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci kungiyar Chelsea, daga bisani kuma ya samu nasara lashe wasanni 13 a jere, wanda kuma a waccan lokacin kungiyar ta Tottenham ad a yanzu yake horaswa ce ta kawo karshen nasarorin da ya jera da kwallaye 2-0.