Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe watanni shida ana yi a Sudan ta Kudu, ya rutsa da mutane akalla dubu 760.
Sanarwar da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya fitar, ya bayyana cewa yanzu haka kasashe 8 daga cikin 10 na kasar Sudan ta Kudu sun fuskanci ambaliyar ruwa, lamarin da ya yi illa ga samar da kiwon lafiya da sauran ayyuka.
Ana cikin wannan hali ne kuma fadan da ake gwabzawa tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai na kabilun kudancin kasar Sudan ta Kudun ya haifar da cikas ga ayyukan bayar da agaji, lamarin da ya tilastawa dubban jama’a neman mafaka a makwabciyar kasar Uganda.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR a watan da ya gabata ta bayyana ambaliyar a matsayin mafi muni da aka gani a wasu yankuna tun shekara ta 1962, inda ta dora alhakin ruwan sama a kan sauyin yanayi.
Ta yi gargadin cewa shekaru uku a jere da aka shafe shekaru uku ana fama da ambaliyar ruwa ta lalata karfin da mutane ke iya jurewa barnar da aka yi.