Adadin mutanen da suka mutu a harin Banibangou ya kai 69

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewar mutane da dama ne suka mutu cikin su harda Magajin Garin Banibangou sakamakon harin da ‘Yan ta’adda suka kai Yankin Tillaberi dake kusa da iyakar kasar Mali da Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu ya kai 69, yayin da 9 suka bata, 15 kuma suka tsira.

Wani dan majalisa daga Yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewar Magajin Garin Banibangou na daga cikin wadanda aka kashe, kuma an samu gawar sa.

Shugaban Nijar Bazoum Mohamed yayin kaddamar da makarantar horas da sojoji a birnin Yamai. 15/10/21 © Mohamed Bazoum

Wannan na daga cikin munanan hare haren da ‘Yan ta’adda ke kaiwa wasu sassan Jamhuriyar Nijar, musamman kusa da iyakar Mali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *