Yadda ta kaya a gasar zakarun Turai ta jiya

Liverpool ta samu gurbi a matakin kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai bayan da ta doke Atletico Madrid da ci 2-0 a jiya Laraba.


Diogo Jota da Sadio Mane ne suka ci wa Liverpool kwallayen biyu a minti na 13 da kuma 21 kuma duk sun samu agaji ne daga Trent Alexander.Atletico Madrid ta karkare fafatawar ta jiya da ‘yan wasa 10 bayan jan katin da aka bai wa mai tsaron bayanta, Felipe na Brazil sakamakon yi wa Mane keta.
Ita ma Ajax ta samu nasarra tsallakawa zuwa matakin kungiyoyi 16 sakamakon nasarar doke Borussia Dortmund da ci 3-1.
Sauran sakamakon wasannin sun nuna cewa, Real Madrid ta doke Shakhtar Donetsk da ci 2-1.
Karim Benzema ne ya ci wa Madrid dukkanin kwallayen biyu, yayin da kungiyar ta ci gaba da zama a saman teburin rukuninsu na D.
Kwallon farko da Benzema ya jefa, ta sanya Real Madrid zama kungiyar farko a Turai da ta zazzaga jumullar kwallaye dubu 1 a raga.
Ita kuwa PSG ta yi canjaras ne 2-2 da RB Leipzig.
PSG ta yi wasan na jiya ne ba tare da Lionel Messi wanda ya samu karamin rauni a ranar Juma’a.
Yanzu haka PSG ta sauko zuwa matsayi na biyu a rukininsu na A, yayin da Manchester City ta dare matsayi na daya bayan da ta lallasa Clube Bruges da ci 4-1.
AC Milan ta yi kunnen doki 1-1 da FC Porto, sai Inter Milan wadda ta casa Sheriff Tiraspol da ci 3-1, yayin da Besiktas ta sha kashi a hannun Sporting da ci 4-0.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *