Sarkin Musulmin Najeriya ya yi bikin cika shekaru 15 kan karaga

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya kuma shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a kasar, Sultan Sa’ad Abubakar ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da zaman lafiya a kasar.

Sultan Sa’ad ya bayyana haka ne a wurin bikin cikarsa  shekaru 15 kan karaga a matsayinsa na Sarkin Musulmi na 20.

Sultan ya bada tabbacin hadin guiwa da al’umma domin bada gudunmawarsu wajen magance dimbin matsalolin da ke addabar Najeriya.

Sheikh Ismael Mufti Menk na Zimbabwe, shi ne bakon da ya gabatar da makala mai taken “ Koyarwar addini da zamantakewa domin samun zaman lafiya a kasashe masu tasowa”

A yayin gabatar da makalar, Menk ya bukaci Musulmai da su guji kyamatar jama’a tare da mutunta sauran addinai.

Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike wa Sarkin Musulmin da sakon taya shi murnar cika shekaru 15 kan karagar mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *