Kasashen Afirka sun bukaci biliyoyin daloli a matsayin diyya

Kasashen Afirka dake fama da illar da matsalolin sauyin yanayin da basu suke haifarwa a duniya ke samarwa, da suka hada da fari da ambaliya da kuma yunwa, na bukatar diyyar biliyoyin daloli a wajen taron sauyin yanayin dake gudana a Glasgow da aka yiwa lakabi da COP26.

Mutane da dama na kallon wannan taron a matsayin wani yunkuri na karshe da ya ragewa shugabannin kasashen duniya wajen daukar matakan ceto Bil Adama da muhallin su daga tabarbarewa.

Abinda ya rataya akan kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya shine batun rage sinadarin da suke fitarwa wadda ke haifar da gurbacewar muhallin da aka akalla maki guda da rabi a ma’aunin salsas, kamar yadda ake da shi kafin shekarun da aka samu karuwar masana’antu a duniya.

Amma ga kasashe irin na Afirka, babban abinda ke gaban su shine samun isassun kudaden da zasu yi amfani da su wajen bunkasa tattalin arzikin su wadanda suka gamu da koma baya sakamakon gurbacewar muhallin, tare da kuma samar da yanayin da za’a ci gaba da rayuwa da matsalolin da ake fuskanta.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU kuma shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Felix Tshisekedi yace nahiyar Afirka ba zata iya shawo kan wadannan matsaloli ita kadai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *