An tabbatar da mutuwar mutane 36 a rushewar benen Lagos

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon rushewar bene mai hawa 21 a jihar Lagos ta Najeriya ya kai 36 ya zuwa yanzu.

Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa a yankin Kudancin Najeriya, Ibrahim Farinloye ya sanar da karuwar alkaluman mamatan, yayin da ya ce, an ceto mutane tara da ransu.

Har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin ceto kamar yadda babban jami’in na  NEMA ya tabbatar.

Rahotanni na cewa, akalla mutane 70 na cikin ginin lokacin da ya rufta da su a ranar Litinin.

A bangare guda, an tabbatar da mutuwar wata budurwa mai bautar kasa, Zaynab Sanni Oyindamola wadda aka fara tura ta jihar Borno, amma mahaifiyarta ta bukaci a mayar da ita Lagos saboda rashin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *