Amurka ta musanta ikirarin Iran kan kwace tankar mai

Amurka ta musanta ikirarin da Iran ta yi  cewa, dakurunta na musamman sun dakile yunkurin kwace mata wani jirgin ruwan daukar danyen mai a tekun Oman da Amurkar ta yi.

Jami’an Amurka da suka yi magana bisa sharadin a sakaya sunayensu, sun ce babu kamshin gaskiya a rahotonna na Iran, saboda  Amurka ba ta yi yunkurin kwace tankar dakon man Jamhuriyar Musuluncin ba.

Sun kara da cewa gaskiyar lamari ita ce, dakarun Iran ne suka karbe wani jirgin ruwan dakon man kasar Vietnam a watan da ya gabata, kuma abin da sojin ruwan Amurka ke yi tun daga wancan lokaci shi ne sintirin sanya ido a kan halin da ake ciki.

A makon da ya gabata ne, Iran ta yi ikirarin cewa dakarunta na musamman sun dakile wani yunkuri daga sojin ruwan Amurka  na kwace mata wata tankar dakon manta makare da danyen mai a tekun Oman.

Zaman tankiya na ci gaba da karuwa tsakanin Tehran da Washington a yayin da aka samu tsaiko a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015, kuma a Larabar nan babban jami’in tsaron kasar Ali Shamkhani ya ce, yarjejeniyar za ta wargaje matsawar shugaba Joe Biden bai bada tabbacin Amurka ba za ta saba alkawari ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *