‘Yan tawayen Habasha sun sha alwashin mamaye Addis Abba

‘Yan tawayen yankin Tigray dake kasar Habasha na iya mamaye birnin Addis Ababa cikin ‘yan watanni ko makonni masu zuwa kamar yadda wata kungiyar Oromo da ke kawance da mayakan Tigray suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP a wannan  Laraba, dai-dai lokacin da mayakan ke ci gaba da kutsawa kudancin kasar.

Kungiyar Tawayen Tigray People’s Liberation Front (TPLF) da ta shafe shekara guda tana yakar gwamnatin Firaiminista Abiy Ahmed, ta yi ikirarin samun gagarumar nasara a mamaye wasu yankuna a ‘yan kwanakin nan, tare da kawayenta na ‘yan tawayen Oromo Liberation Army (OLA).

Odaa Tarbii, mai magana da yawun OLA, wanda kuma ya yi ikirarin ci samun ci gaba a baya-bayan nan a Amhara da kuma yankin Oromia da ke kewaye da Addis Ababa, ya ce kungiyarsa ta yi niyyar hambarar da gwamnatin Abiy Ahmed, yana mai cewa korar sa abu ne da sukayi nisa akai.

“Idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a halin yanzu, to muna magana ne kan batun watanni idan ba makonni ba,” in ji shi,

Kalaman na zuwa ne sa’o’i bayan kasar Habasha ta ayyana dokar ta-baci a fadin kasar a ranar Talata tare da bada umurni ga mazauna birnin Addis Ababa da su shirya don kare matsugunan su.

A cikin wata sanarwa da ya fitar wannan Laraba, Abiy ya zargi kawancen ‘yan tawayen da kokarin mayar da Habasha tamkar kasar Libya da Syria, yana mai cewa: “Sun shirya ruguza wata kasa – ba wai su gina ta ba.”

Ya kuma bukaci ‘yan kasar da su goyi bayan yakin, yana mai cewa: “Nasara kan barazanar da makiyanmu ke yi ba zai yiwu ba idan ba a hada kai ba.”

A karkashin dokar ta-baci, hukumomi na iya daukar duk wani dan kasa da shekarunsa ya kai ga aikin soji, tare da dakatar da duk wani kafar yada labarai da aka yi imanin cewa “na goyon baya kai tsaye ko a kaikaice” ga kungiyar tawayen TPLF, a cewar Fana Broadcasting Corporate mai alaka da gwamnati.

A wannan Laraba ake sa ran ‘yan majalisar su amince da dokar ta bacin, in ji Fana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *