‘Yan bindiga sun sace malaman jami’ar Abuja

‘Yan bindiga sun sace malaman jami’ar Abuja da ke Najeriya a sanyin safiyar yau Talata, inda suka shafe tsawon sa’o’i biyu suna cin karensu babu babbaka kamar yadda shaidu suka bayyana.

Jami’an ‘yan sandan birnin Abuja sun tabbatar da aukuwar lamarin .

A cikin wata sanarwa, kwaminishinan ‘yan sandan Abuja Babaji Sunday ya ce, tuni ya tura karin kwararrun jami’ai zuwa jami’ar ta UNIABUJA.

Binciken farko na nuni da cewa, ‘yan bindigar sun sace mutane 6 kuma sun yi cikin daji da su.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka baza dakarun kasar zuwa wasu jihohi irinsu Zamfara domin yaki da ‘yan bindigar masu garkuwa da jama’a suna karbar kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *