Yadda mata 3 suka bar kasashensu na turai suka kauro Afrika, Najeriya

Wasu daga cikin wadannan matan sun sami kansu a Afirka kwatsam kuma sun kaunaci nahiyar, amma ga wasu, shawara suka yanke su dawo Afrika dindindin.

Wasu mata turawa guda 3 da gangan ko kuma kwatsam suka tsinci kansu a kasashen Afirka amma suka so ta suka dauke ta a matsayin gida.

1.Juliana Belova

Juliana Belova na daya daga cikin ‘yan matan da suka yanke shawarar da ba kowa ne zai iya ba.

Baturiyar ta tattara kayanta ta yanke shawarar zuwa Nigeria bata waiwaya ba tun daga nan.

Baturiyar ‘yar kasar Rasha wadda aka fi sani da suna Oyinbo Marlian a Najeriya ta bar kasarta zuwa Najeriya da N41,000 kacal.

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta yanke shawarar da ba a saba gani ba, Juliana ta ce ta bar kasar Rasha ne saboda sha’awarta da wasan kwaikwayo na Najeriya.

Tana daya daga cikin masu kirkirar wasannin kwaikwayo na ban dariya a Najeriya a halin yanzu.

2. Thessa Bagu

A daya bangaren kuma Thessa Bagu ta zauna a Najeriya tun shekaru 15 da suka gabata amma ba haka kawai ba.

A cewar matar ‘yar kasar Holland, ta zo Najeriya ne a shekarar 2006 domin hutun shekaru 2, amma ta kasance tana son kasar da al’ummarta.

Ta ce kasar ta sauya rayuwarta zuwa ga mai kyau duk da kalubalen da ta ke fuskanta.

3. Stephanie Fuchs

Ga Stephanie Fuchs, soyayya ta fada, amma ba a Najeriya ba – a Tanzaniya.

Matar Bajamushiya wacce ta dira Tanzaniya a shekara ta 2011 a matsayin ma’aikaciyar bincike a wani sansani, amma ta kamu da soyayya da wani mutum dan kasar.

2 Replies to “Yadda mata 3 suka bar kasashensu na turai suka kauro Afrika, Najeriya”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *