Ronaldo ya ceto Manchester United a wasan da sukayi 2-2

Ronaldo ya ceto Manchester United a wasan da sukayi canjaras 2-2 da Atalanta a gasar zakarun Turai ranar Talat.

Wannnan dai shine karo na 3 da Cristiano Ronaldo ke ceto Manchester United a irin wannan yanayi a makare a wasanni hudu na gasar zakarun Turai.

Dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a gasar, ya burge kungiyar da magoya baya wajen rama kwallon karshe ana daf da tashi daga wasa, tare da taimakawa kungiyar ci gaba da kasancewa saman teburin rukunin F.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *