Robert Lewandowski ya doki wasansa na 100 cur a gasar zakarun Turai, tare da cin kwallo uku da ake kira hat-trck a wasan da kungiyar sa ta Bayern Munich ta lallasa Benfica da ci 5-2 daren Talata tare da darewa zagayen ‘yan 16 na gasar Champions League.
Lewandowski da Serge Gnabry da Leroy Sane ne suka ci wa Bayern kwallaye a filin wasa na Allianz Arena yayin da Morato da Darwin Nunez suka ci wa Benfica kwalloye biyu.
Lewandowski, wanda ya barar da bugun finareti a wasan na ranar Talata, a yanzu ya zura kwallaye 81 a gasar zakarun Turai a wasanni 100 da ya doka a gasar zakarun Turai tun daga lokacin da ya fara wasa a tsohon kulob dinsa Dortmund shekaru goma da suka wuce.

Nasarar hudu a jere da Bayern ta samu ya ba ta damar hayewa zagayen ‘yan 16 na gasar da sauran wasannin rukuni guda biyu, inda suka kasance saman teburin rukunin E da maki 12, shida tsakanin ta da Barcelona dake biye mata da maki 6.