Kasashe sun sha alwashin rage hayaki mai guba da kashi 30 nan da shekarar 2030

Sama da kasashe 80 ne suka rattaba hannu kan yerjejeniyar magance matsalar dumamar yanayi, ta hanyar rage hayakin sinadarin methane da kashi 30 cikin dari nan da karshen shekaru goma masu zuwa.

Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen  ta ce mayar da hankali sosai kan yadda za a rage amfani da wannan sinadari da kashi uku cikin rubu’I na ukun shekarar 2020 zai yi saurin rage matsalar dumamar yanayin da ake fama da ita a halin yanzu.

Ta ce kusan kashi 30 na dumamar yanayin da ake fama da shi ya samo asali ne tun bayan bullowar  masana’antu wanda ake ganin sinadarin na methane ne yake janyo hakan.

Ursula Von der Leyen ta ce hayakin methane yana karuwa da sauri fiye da kowane lokaci a baya, inda tace rage karfin methane na daya daga cikin abu mafi muhimmancin hanyoyin rage dumamar yanayi da kuma cimma burin da ake kwadayi na rage zafin yanayi da daya da rabi na ma’aunin Celsius.

Wannan fatan dai na zuwa ne kwana guda bayan Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki shugabannin da suka taru domin daukar matakin ceto bil adama, ta hanyar rage amfani da abubuwan da ke haddasa dumamar yanayi a doron kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *