Adams ya zama bakar fata na biyu da ya lashe zaben magajin garin New York

An zabi Eric Adams, bakar fata a matsayin magajin garin birnin New York na Amurka kamar dai yadda alkalumman karshe da kafafen yada labaran kasar ciki har da CBS da kuma NBC suka bayyana.

Eric Adams na jam’iyyar Democrat, wanda tsohon jami’in ‘yan sanda ne ya lashe zaben ne ta hanyar doke abokin hamayyarsa Curtis Sliva na jam’iyyar Republican, inda ya zama bakar fata na biyu da ya yi nasarar kasancewa magajin garin New York karo na biyu a tarihi.

Alkalumman da kafafen yada labarai suka fitar jim kadan bayan kammala kada kuri’a na nuni da cewa Adams mai shekaru 61 a duniya, ya samu 70% yayin da abokin hamayyarsa ya samu 23%.

Sabon magajin garin kuma tsohon jami’in ‘yan sanda, ya gudanar da yakin neman zabensa ne ta hanyar nuna jajircewa da kuma yin tir da wariya da ‘yan sanda ken una wa jam’a a Amurka.

Eric Adams wanda zai fara aiki cikin watan Janairu mai zuwa amastayin sabon magajin garin birnin New York na da manyan kalubale a gabansa, musamman kokarin farfado da tattalin arziki da kuma kare lafiyar mazauna New York birnin da aka samu asarar rayukan mutane sama da dubu 34 sakamakon annobar covid 19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *