A Najeriya Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ce an samu karin wasu gawarwakin mutane biyu da aka fitar da sanyin safiyar wannan Laraba daga baraguzan dogon bene da ya ruguje a birnin Legas, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 22.
Ana ci gaba da aikin ginin mai hawa 21 kafin ruftawarsa ranar Litinin da ta gabata a unguwar Ikoyi da ke cibiyar kasuwancin Najeriya.
Masu aikin ceto sun ce a ranar Laraba sun gano gawarwaki 22 ya zuwa yanzu tare da ceto mutane tara da suka tsira, amma masu aikin ginin na fargabar har yanzu akwai abokan aikinsu da dama da suka makale a ciki.
Babu tsammani samun masu rai
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Lagos, Ibrahim Farinloye yace, Fatan samun karin wadanda dake da sauran numfashi ya ragu, yayin da aka shiga kwanaki na uku wannan Larana ana aikin ceto.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun kai ga matakin kasa,” in ji Farinloye, ya kara da cewa an kawo manyan kayan aiki a yammacin ranar Talata domin gudanar da aikin.
A baya dai ya ce ma’aikatan ceto na tattaunawa da wasu da ke makale a karkashin ginin da ya ruguje.
Dangi na dandanzo harabar ginin
‘Yan uwa da abokan arziki da abin ya rutsa da su sun yi dandazo tun a ranar Litinin din da ta gabata, domin neman bayani kan makomarsu.

Rushewar gine-gine na neman zama ruwan dare
Rushewar gine-gine dai ya zama ruwan dare a Legas da ma kasar mafi yawan al’umma a Afirka inda rashin ingancin kayan aiki, sakaci da rashin aiwatar da ka’idojin gine-gine su ne manyan matsaloli.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce lokaci baiyi ba da za a tantance dalilin da ya sa ginin na Ikoyi ya ruguje, amma shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Legas Femi Oke-Osanyintolu ya ce an tafka kura-kurai wajen kafa tubalin ginin.