Tedros ya kama hanyar samun wa’adi na 2 a Hukumar Lafiya

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya kama hanyar ci gaba da jagorancin ta a wa’adi na biyu da zaran wa’adin sa ya kare saboda rashin samun abokin takarar jagorancin Hukumar.

Sanarwar da Hukumar ta gabatar yace bayan cikar wa’adin gabatar da ’Yan takarar jagorancin Hukumar ta Lafiya a ranar 23 ga watan Agustan wannan shekara, babu wani ‘dan takarar da ya gabatar da bukatar sa, sai Gebreyesus wanda kasashe 28 suka gabatar da sunan sa domin ci gaba da jagorancin Hukumar sakamakon rawar da ya taka wajen shawo kan matsalar annobar korona.

Daga cikin kasashen da suka goyi bayan shugaban domin ci gaba da jagorancin Hukumar akwai kasashen Turai 17 da suka hada da Austria da Faransa da Jamus da Netherlands da Portugal da Spain da Sweden da kuma ita kan ta kungiyar EU.

Alamar Hukumar Lafiya ta Duniya Fabrice COFFRINI AFP/File

Kasashen Jamus da Spain sun ce goyan bayan Gebreyesus zai taimaka wajen shawo kan annobar korona ba tare da raba hankali ba, ganin yadda Hukumar ke bukatar jajircewa da jagoranci na gari irin na shi.

Daga cikin kasashen da suka goyi bayan takarar shugaban a wajen nahiyar Turai kuma akwai kasashen Bahrain da Barbados da Botswana da Tsibirin Cook da Indonesia da Kazakhstan da Kenya da Oman da Rwanda da Tonga da kuma Trinidad da Tobago.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *