Ole Gunnar Solskjær ya ce zai iya yin koyi da Sir Alex Ferguson wajen dagewa don ganin ya fita daga matsalar da yake fuskanta a matsayinsa na kocin Manchester United har ma ya iya kai kungiyar ga nasarori.
Aikin dan kasar Norway din yana tangal tangal tun bayan da Liverpool ta yi wa U ited dukan kawo wuka 5-0, har gida.
Duk da cewa Solskjær ne zai jagoranci kungiyar zuwa gidan Tottenham a ranar Asabar, babu tabbacin cewa zai ci gaba da kasancewa kocinta na tsawon lokaci.
Shi ma Ferguson sai da ya rage kiris a kore shi a matsayin kocin kungiyar a shekarar 1990 bayan da ya shafe sama da shekaru 3 ba tare da lashe kofi ba, amma sai ya tsallake rijiya da baya, inda a watan mayun shekarar ya lashe kofin kalubale, har ma ya shafe shekaru 23 tar