Sojojin Sudan sun sallami jakadun wasu kasashe 6 daga kasar

Sojoji a Sudan sun bada sanarwar sallamar jakadun wasu kasashe 6, a dai-dai lokacin da suke kara zage damtse wajen tabbatar da tsaro da kuma shawo kan masu zanga-zangar nuna adawa da juyin mulki, wadda ta juye zuwa tarzoma a kasar.

Matakin sallamar Jakadun na zuwa ne daidai lokacin kasashen duniya har ma da majaliar dinkin duniya ke kara matsa wa sojojin lamba da su gaggauta sakin Firayim Ministan kasar Abdallah Hamdok da suke tsare da shi.

Kasashen da sojojin suka sallami jakadun su daga kasar sun hadar da Amurka da China da Qatar da Faransa da Switzerland sai tarayyar Turai, abin da ake ganin ya faru ne saboda yadda suka yi tir da juyin mulkin.

Bayanai sun ce tuni sojoji suka fara amfani da karfin tuwo wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da su, ta hanyar bude wuta, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7, kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar, bayan mutane sama da dari da suka jikkata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *