Sojin Habasha na ta ci gaba da luguden wuta ta sama kan ‘yan tawaye dake yankin Tigray na kasar, inda majiyoyi masu tushe ke cewa rayukan mutane 10 aka salwantar a Alhamis kawai.
A cewar Gwamnatin kasar, hare-haren ta sama ta kai shi ne a wata masana’anta dake Mekele inda ‘yan kungiyar ‘Yantar da al’ummar Tigray wato Tigray Peoples Liberation Front TPLF, ke amfani da shi.
Dr Hayelom Kebede , Daraktan a asibitin Ayder dake Mekele ya ce harin ya shafi asibitin, kuma an yi barna, domin mutane 10 sun mutu wasu 21 kuma suka sami raunuka.
Ma’aikatar harkokin sadarwa na yankin Tigray ta ce a na ta bangaren an sami barna a rukunin gidajen kwana na ma’aikata.
Tun da fari kakakin kungiyar ta ‘yantar da al’ummar Tigray, ta hannun kakakinta Getachew Reda ta sanar da cewa lallai sun yi hasarar rayukan mutane a harin da sojan Habashan suka kai ta sama.