Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Juma’a ya ce bai yanke shawarar fitowa takarar shugabancin kasa a 2023 ba.

Kwankwaso ya kara da cewa, gwamnonin jihohi ba za su iya zama a Legas ko wani wuri a arewa ba su yanke shawarar wanne yanki ne zai samar da shugaban kasa na gaba ba.

Ya ce wannan hukuncin jam’iyyun siyasa ne kadai za su iya yanke wa bayan duba duk abubuwan da suka dace, ya kara da cewa abinda ya fi dacewa kuwa shi ne samun mutumin da ya fi dacewa da shugabancin.

Tsohon gwamnan ya sanar da hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi da gidan talabijin na AriseTV, inda ya caccaki mulkin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana cewa sam bai gamsu da tsarin mulkin Ganduje ba. Ya caccaki tsarin jihar na cin bashi mai tarin yawa inda ya ce a halin yanzu jihar Kano na dawainiya da bashin da ya kai N187 biliyan wanda kuma bai dace.

A yayin da aka tambaye shi ko zai fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2023, ya ce, “Ban riga na yanke wannan shawarar ba.”

One Reply to “Gwamnoni ba su da hurumin ayyana yankin da zai samar da shugaban kasa, Kwankwaso”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *