Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace babu abinda zai sa shi ci gaba da zama a karagar mulki bayan ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023, idan wa’adin mulkin sa ya cika, inda yayi watsi da masu yada jita-jitar tsawaita wa’adin gwamnatin sa.TALLAhttps://be953e60b56d1da8565a6d330ab8a94e.safeframe.googlesyndication.com/safeframe/1-0-38/html/container.html
Yayin da yake ganawa da wasu ‘Yan Najeriya a birnin Makkah dake Saudi Arabiya inda ya kai ziyara, shugaban yace ba shi da wata aniya ta yin ‘Tazarce’ kamar yadda ya rantse da Al Kur’ani na kare kundin tsarin mulki, kuma baya bukatar wani mutum ya fara tsokaci akai ko kuma fara neman goyan bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar, inda yake cewa ba zai taba amincewa da hakan ba.
Buhari ya kuma bayyana goyan bayan sa dangane da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da harkokin zaben kasar, inda ya bayyana cewar gabatar da na’urar tantance masu kada kuri’u da kuma rajistar masu zabe wajen amfani da na’ura na daga nasarar amsa addu’o’in sa da Ubangiji yayi saboda magudin da aka masa har sau 3 a zabukan da suka gabata.
Bayan abinda ya kira faduwar da yayi har sau uku a zabukan kasar, Shugaban ya mayar da al’amarin sa ga Ubangiji, yayin da abokan hamayar sa suka yi ta masa dariya, amma sai Allah Ya amsa addu’ar sa wajen gabatar da fasahar zamanin da akayi amfani da su wadanda suka hana satar kuri’u da kuma sayar da su.

Sanarwar da mai magana da yawun sa Garba Shehu ya rabawa manema labarai tace shugaban ya kammala ziyarar Saudiya da halartar Sallar Juma’a a Masallachin Ka’aba, inda ya jaddada aniyar sa ta ci gaba da mutunta kundin tsarin mulki ta kowane fanni da kuma sanya ido wajen ayyukan da ministocin sa keyi kamar yadda doka ta tanada.PUBLICITÉ
Sanarwar tace Buhari ya jaddada aniyar sa ta ci gaba da ayyukan da zasu inganta rayuwar ‘Yan Najeriya a cikin watanni 18 da suka rage na mulkin sa.

Shugaban ya kuma bukaci Yan Najeriya da su yiwa gwamnatin sa adalci a koda yaushe, inda ya bukaci masu sukar su da su kwatanta halin tsaron da ake ciki a Yankin Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu a shekarar 2015 da yadda al’amura suka sauya yanzu.
Buhari yace damuwar sa itace Yankin Arewa maso Yamma inda mutane ke kashe ‘Yan uwan su suna sata, abinda ya sa ya dauki mataki mai tsauri akan su, inda ya kara da cewar zai ci gaba da daukar irin wadannan matakai har sai an dawo da doka da oda a yankin.