Amurka tayi alkawarin taimakawa Jamhuriyar Nijar

Kasar Amurka ta bayyana aniyar ta na aiki tare da Jamhuriyar Nijar wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabe kasar da kuma yankin Sahel baki daya.

Jakadan Amurka a Yammai Eric Whitaker ya bayyana haka, bayan ganawar da aka yi tsakanin shugaba Bazoum Mohammed da mai baiwa shugaban Amurka Joe Biden shawara akan tsaron cikin gida, Dr Elizabeth Sherwood-Randall da kuma kwamandan rundunar tsaron Amurka dake kula da Afirka, Janar Stephen Townsend.

Whitaker yace Amurka ta taya shugaba Bazoum nasarar zaben da ya samu da kuma tarihin da Nijar ta kafa na mika mulki daga zababben shugaba zuwa wanda ya gada ba tare da samun wata matsala ba.

Janar Townsend ya shaidawa shugaba Bazoum cewar rundunar sojin Amurka a shirye take tayi aiki kafada da kafada da sojojin Nijar domin tabbatar da tsaro a kasar da kuma Yankin Sahel.

Jakadan Amurka yace bayan matsalar tsaro, bangarorin biyu sun kuma tattauna akan batutuwan ci gaba da dimokiradiya da kuma diflomasiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *