China ta bullo da sabon tsarin rage hayaki mai guba

China ta dukufa wajen rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli ta hanyar inganta makamashi mai sabantuwa na zamani nan da shekara ta 2030 kamar yadda Majalisar Ministocin kasar ta sanar.

Sabon matakin tamkar nanata kudirin da China ke son cimma ne na daidaita karfin iska da na rana zuwa gigawatts dubu 1 da 200 nan da shekaru 10 masu zuwa domin gina karin cibiyoyin samar da wutar lantarki da nukiliya.

Wadannan bayanai da China ta fitar na zuwa ne kwanaki kalilan gabanin fara babban taron sauyin yanayi a birnin Glasgow da aka shirya domin karfafa wa kasashen duniya guiwa wajen yaki da matsalar dumamar yanayi.

Manzarta kan sauyin yanayi sun jima suna sanya wa China ido wadda ke zama kasar da ta fi kowacce a duniya fitar da gurtabacciyar isa.

Ana sa ran kasar ta China za ta sake gabatar da wasu alkawura nan gaba dangane da rage dumamar yanayin kafin soma taron na birnin Glasgow.

A halin yanzu dai China na fama da matsalar karancin lantarki, yayin da ta dukufa wajen samar da gawayi domin ci gaba da rarraba lantarkin babu kakkautawa a lokacin hunturu, yayin da Majalisar Ministocin kasar ke cewa, za su kara kaimi wajen gina sabuwar cibiyar samar da makamashi na zamani kuma mara gurbata muhalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *