Bayern Munich ta sha mummunan kashi irinsa na farko tun shekara ta 1978, bayan da Borussia Monchengladbach ta yi mata yayyafin kwallaye 5-0 a gasar cin kofin Jamus.
Cikin minti biyu da saka wasan ne, Monchengladbach ta fara farke ragar Bayern Munich, sannan kafin minti 21, kungiyar ta zazzaga kwallaye uku.
Tuni jiga-jigan Bayern Munich suka bayyana kaduwarsau ta wannan rashin nasara, inda darektan wasanni na kungiyar, Hasan Salihamidzic ya ce, ko kadan ba su tabuka abin kirki ba.
Raban da a yi wa Bahyern Munich irin wannan zazzagar kwallayen tun shekaru 47 da suka gabata, lokacin da Fortna Dusseldorf ta doke su da ci 7-1 a gasar Bundesliga a wancan lokaci.