Barcelona ta sallami kocinta Koeman

Barcelona ta sallami kocinta Ronald Koeman bayan ya shafe tsawon watanni 14 yana jagorancin kungiyar a Camp Nou.

Wannan na zuwa ne bayan Barcelona ta samu maki 15 kacal daga cikin jumullar wasanni 10 da ta buga a gasar La Liga, yayin da ta yi rashin nasara har sau biyu a matakin wasannin rukuni a gasar zakarun Turai.

Yanzu haka Barcelona na matsayi na 9 kan teburin La Liga, inda take kasan Real Madrid ta Sevilla da suka bata ratar maki 6.

A jiya Laraba, Barcelona ta sha kashi a hannun Rayo Vallecano da ci 1-0 a gasar ta La Liga, kuma sau uku kenan da take shan kashi a wasanni hudu da ta buga a baya-bayan nan.

A yau Alhamis ne Koeman zai yi wa kungiyar ta Barcelona bankwana a hukumance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *